Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a sa mince meat a kwano, sai a sa sinadarin dandano, da dan gishiri, a sa tafarnuwa da markadadden albasa da tarugu, sai a sa digon Mai a non stick frying pan, sai a diba mince meat din ayi flattening din shi, a sa a pan din, a danna da spoon yayi flat, in side din yayi, sai a juya dayan side din yayi dark brown.
- 2
Sai a wanke vegetables din, ayi slicing dinsu
- 3
Sai a yanka burger bread din Kashi biyu, sai a dauko ganyen latas a daura a kan gefe daya, sannan a dora tumatir a Kai, sai a dauko minced meat din da aka gasa a dora a Kai, sai a sa cucumber, tumatir, sannan wani ganyen latas, sai a dauko dayan barin bredin a rufa a sama, shikenan burger ya hadu. (Ana sa cheese a burger, amma ni bansa ba).
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10820058




sharhai