Gasasshen meat pie

Ina matuqar son meat pie sosai d sosai hakanne yasa nake yawan yinshi sosai amma wannan ya banbanta da sauran wanda nakeyi domin yayi dadi na ban mamaki #FPPC
Gasasshen meat pie
Ina matuqar son meat pie sosai d sosai hakanne yasa nake yawan yinshi sosai amma wannan ya banbanta da sauran wanda nakeyi domin yayi dadi na ban mamaki #FPPC
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na soya nama nasa karas, albasa da kayan kamshi d dan dano sena ajiye shi gefe.
- 2
Sena tankade flour dita nasaka, gishiri, sugar, baking powder d butter na jujjuya har komai y hade
- 3
Sena tumeric kadan Don yabashi kala mai kyau sena sa ruwa na kwaba dough dina na rufeshi d leda na minti 20 don ya hade jikinsa.
- 4
Bayan haka sena dakko na murza nasa abu mai circle na fitar d shape din sena dau daya nasaka hadin naman a tsakiya na shafa ruwa a gefe
- 5
Sena dau wani na rufe wanda nasa naman nasa fork na daddanne, haka na tayi har nagama.
- 6
Sena fasa kwai n shafa sannan na gasa na tsawon minti 20
Similar Recipes
More Recipes

sharhai