Kosan dankalin turawa

Lokaci zuwa lokaci ina yiwa iyalai na abincin bazata sbd faran ta musu a ko d yaushe nayi wannan Kosan dankalin turawa ne sbd su kuma sunji dadin shi sosai kuma sunyi nishadi sosai sbd wannan hadadden girki na musamman danayi musu sun karfafafin gwiwa sosai akan Cookpad wannan abun yy min dadi sosai 😋😋😋 ki gwada kawai kisha mmki #FPPC

Umarnin dafa abinci
- 1
Wannan sune abubuwan da muke bukata wajen yin Kosan dankalin turawa
- 2
Da farko zaki fere dankalin turawa saiki dafa shi idan y nuna saiki sauke ki zuba a turmi ki dakashi b sosai ba sai ki dafa namanki d Maggi gishiri da albasa da kuma kayan kamshin girki idan y nuna saiki sauke ki daka shi ki jajjaga attaruhu tattasai albasa tafarnuwa sai ki zuba su duka a kwano daya mai tsafta ki saka maggi gishiri kadan d kuma kayan kamshin girki
- 3
Saiki hade su baki daya sai kinga sun hade jikin su
- 4
Sannan saiki mulmulashi zuwa kwallo
- 5
Saiki saka a cikin kwai
- 6
Sannan ki cire kisa a cikin fulawa
- 7
Idan mai dinki Yy zafi saiki zuba wannan Kosan dankalin turawa a ciki ki soya shi idan yy ruwan kasa saiki kwashe
- 8
A zuba aci d iyalai 😋😋 kuyi girki cikin farin ciki 😍😘
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai