Tsire

zhalphart kitchen @cook_15662647
Inason nama shiyasa nake sarrafashi ta hanyoyi da dama💯 #FPPC
Tsire
Inason nama shiyasa nake sarrafashi ta hanyoyi da dama💯 #FPPC
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki jika tsinkenki a ruwa yayi awa daya (sbd bazaiyi kamu ba kuma tsinken bazaiyi baki ba gurin gashi)
- 2
Zaki yanka namanki yayi fadi saiki zuba acikin bowl kisa garin barkono,garin tafarnuwa,Maggi,gishiri kadan saiki juya saiki kawo kuli kuli ki zuba ki juya sosai
- 3
Saiki zuba mai ki juya sosai ki rufe ki barshi awa daya,bayan awa daya saiki dakko tsinke ki jera ajiki
- 4
Zaki samu wani plate ki zuba kuli kuli,Maggi,garin barkono ki juya sosai saiki dinga dakko naman kina sawa ajiki ko Ina yaji saiki jera a akan abin gashi ki shafa mai da brush shikenan saiki gasa
- 5
Shikenan kin gama😋😋dadi baa magana💯
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12606707
















sharhai