Steps
- 1
Idan kika samu waken awara sai ki wankesa da kyau ki fitarda tsakuwa da sauran kazanta saiki jika like 15munute sai ki markada(nika)
- 2
Idan an niko(markado) saiki zuba ruwa ki tace shi a cikin tukunyarda zaki dafashi ciki kada a bari dussa ta shiga sai ki daura kan wuta
- 3
Idan kin aza kan wuta saikiyo kusa da ruwan yaminki ko ruwan alif ko ruwan tsamiya kode dami zakiyi Abu mai yami(Tami)ake bukata
- 4
Idan yaji wuta zakiga yana tasowa yana borowa duk kikaga ya taso saiki zuba ruwan yamin haka zaki kamayi Sai kega yayi gumba zakiga duk kulun ya debe ya koma ruwa farare
- 5
Daga ban saiki kwashe ki samu abinda zaki darme ruwa su tsiyaye misali cikin buhu empty ko kyalen taci ki dannesa da Abu mai nauyi Sai ruwa ya fita
- 6
Idan ruwan ta tsaye saiki yayyanka daidai girmanda kike son sa
- 7
Zaki jika magi da Dan gishiri kadan ruwa kadan zaki zuba saiki kama dauko yankakken awarar(kwai da kwai)kina sakawa a ruwan Magi
- 8
Saiki aza man gyara/okey a wuta idan yayi zafi saiki soya awarar
- 9
Zaki yanka Kayan lambunki e.g kabbage cucumber saiki jajjaga tattasai tarugu da albasa
- 10
Saiki saka mai a wuta ki saka jajjagen dasu Kayan lambu duka kisa magi da Kayan kanshi
- 11
Idan sauce din ba hadu sai a hada da awarar sai ci
Similar Recipes
More Recipes
-

Pabi Chettri
-

Shobha Deshmukh
-

Shobha Rathod
-

ZMA
-

Kshama's Kitchen
-

Yadnya Desai
-

Radhika Shaparia
-

summerplace
-

Boca de Fogo
-

summerplace
-

Boca Brad -

summerplace
-

rukayya habib
-

rukayya habib
-

rukayya habib
-

rukayya habib
-

summerplace
-

summerplace
-

mariya Mukhtar shehu -

mariya Mukhtar shehu













Comments