Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara kayan miyanki tumatur, tarugu, tattasai da Albasa ki markada,idan kin markada saiki ajiye gefe.
- 2
Ki fere doyarki ki yankata Kanan saiki wanke ki dora a wuta, kibarta tayi rabin dafuwa saiki sauke ki ajiye gefe daya,
- 3
Zaki saka manjanki a wuta ki yanka albasa da tafarnuwa ki soya sama-sama saki saka kayan miyanki ki rufe.
- 4
Idan kayan miyan ya soyu saiki saka Maggi gishiri dadai sauran kayan dandano, ki juya sosai saki saka ruwa kadan daidai yanda zai ida dafa doyan,saiki juye doyan ki rufe.
- 5
Zaki yanke alanyafunki ki wanke saiki saka masa tafashesshen ruwan zafi ki rufe zakiga yayi green sosai Kuma yayi laushe saiki tsiyaye ruwan ki saka alanyanfun a cikin doyan ki rufe ki rage wuta kibarshi ya qarasa dafuwa saiki sauke aci lfy. Zaki iya saka kifi idan kina buqata
Similar Recipes
More Recipes




sharhai