Parpesun naman rago
#parpesurecipecontest naman rago yana da matukar amfani a jikin dan adam,yana cikin nau'in abincin gina jiki,saboda haka yana da kyau a kalla koh sau daya ne a sati aci naman rago. Parpesun naman rago yana da matukar dadi barin idan yaji kayan hadi,parpesun naman rago zaa iya ci da breadi,shinkafa koh taliya da abubuwa da dama. Ina son parpesun naman rago sosai sbd yana da dadi barin in yayi yaji.

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaa dauko nama a wanke shi sosai
- 2
A dauko albasa guda daya a bare da attaruhu guda 3 a wankesu, a yanyanka albasa, a zuba attaruhu a turmi a daka
- 3
A zuba albasar da aka yanka da attaruhun da aka daka a cikin naman rago
- 4
A zuba kayan kanshi da sinadarin dandano
- 5
Sai mu daura naman mu a kanhuta mu zuba tafasheshen ruwan zafi ma daidaici,a zuba mai cokali biyu sai a rufe a barshi ya dafu sosai sbd naman rago in ya dahu sosai yafi dadi
- 6
A dauko ragowar albasa,attaruhu,karas da koran tattasai a wankesu a yanyanka
- 7
Idan nama mu ya dafu sai a zuba kayayyakin da muka yanka
- 8
Sai a rufe a barshi ya kara minti 5 zuwa 10 sai a sauke, parpesun naman rago ya kammala
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai