Irish with Scrabble egg

Ummu Khausar Kitchen @1987kau
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki feraye dankalinki ki wanke shi, saiki yanka ki zuba gishiri kadan saiki dora frying pan dinki a wuta ki zuba mai yayi zafi saiki soyashi. idan ya soyu sai ki kwashe ki ajiye.
- 2
Saiki dauko attarihunki da albasa da tumatir ki yankasu kanana kidora frying pan a wuta ki zuba aciki kisa mai kadan acikin kidan ringa juyawa barshi kadan a wuta.
- 3
Saiki zuba sinadarin dandandano da curry aciki ya dan soyu sama sama.
- 4
Saiki fasa kwai aciki kita juyawa har saiya soyu.
- 5
Sai ki dauko wannan soyayyan dankalin nan ki zuba aciki ki juya har sai ya kama jikin Irish din ki rufe, saiki rage wutan ki, idan yayi saiki sauke.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8986716



sharhai