Soyayyen dankalin Hausa da sauce din kwai

teema habeeb
teema habeeb @cook_14150092

Alokacin sahur inason cin abu marar nauyi sai na hadashi da tea yanamun dadi hakan. #sahurrecipecontest

Soyayyen dankalin Hausa da sauce din kwai

Alokacin sahur inason cin abu marar nauyi sai na hadashi da tea yanamun dadi hakan. #sahurrecipecontest

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

awa da arbain
6 servings
  1. Dankalin
  2. 5dankalin hausa
  3. Gishiri
  4. Mai don soyawa
  5. Sauce din kwai
  6. 2tarugu
  7. 2tattasai
  8. 1albasa
  9. 2maggi
  10. 4kwai
  11. Gishiri kadan
  12. Mai bada yawaba

Cooking Instructions

awa da arbain
  1. 1

    Wannan dankalin Hausa kenan,zaki wankeshi,sannan saiki fereshi da kyau

  2. 2

    Saiki yankashi iya girman da kikeso kamar haka,saiki barshi cikin ruwa harzuwa lokacinda zakiyi amfani dashi

  3. 3

    Saiki tsiyaye ruwan da keciki kisa gishiri kadan ki motsa

  4. 4

    Saiki aza mai yayi zafi kizuba dankalin aciki karki dinga motsawa akai akai,sai dai kibari sai ya kusan soyuwa saiki motsa,kibarshi ya soyu

  5. 5

    Sauce din kwai,zaki ayayyanka tarugu,tattasai,da albasa saiki fara soyasu,ki saka maggi da gishiri saiki yita motsawa har su soyu

  6. 6

    Idan yayi saiki fasa kwai kisa gishiri kadan sai kizuba kibarshi kamar minti daya saiki motsa haryayi

  7. 7

    Sai kiyi serving dankalinki da kwai kici

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
teema habeeb
teema habeeb @cook_14150092
on

Comments

Similar Recipes