Alala da vegetable sauce
Umarnin dafa abinci
- 1
Xaki samu wakenki ki gyara shi ki surfe ki wanke ki fitar da dusa
- 2
Ki hada markaden waken da attauhu da albasa
- 3
Idan an markada sae ki xuba manja, kayan qamshi, maggi, sae ki yanka dafaffen kwai ki xuba a ciki
- 4
Sae ki daura hadadden alalan naki a Santana leather, amma ba'a son a matse shi sossai
- 5
Sae ki daura ruwa a cikin tukunya, idn ya tafasa sae ki saka alalan da kika daura a leather
- 6
Sae ki daidaita wuta ki dafa shi na tsahon miti 10 suwa 15
- 7
Bayan nan, sae ki yanka cabbage da albasa dinki medium size
- 8
Sae ki xuba mai a cikin tukunya ki daura a kan wuta
- 9
Idn yyi xafi sae ki xuba dakakken namanki a ciki
- 10
Sae kisa kayan qamshi da maggi daidai test dinki
- 11
Sae ki dauko yankakken cabbage dinki da albasa ki xuba a ciki
- 12
Sae ki rage wuta sossai su dahu a natse na minti 5 zuwa 10
- 13
Sae ki sauke alalanki ki bareshi daga leather, ki xuwa a plate da vegetable source dinki
- 14
Aci dadi lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai