Dambun couscous

Couscous yana da dadi shiyasa nayi danbushi domin sauki
Dambun couscous
Couscous yana da dadi shiyasa nayi danbushi domin sauki
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na zuba couscous dina a mazubi sena zuba mishi ruwan zafi daidai kanshi da mai senarufe tsawan minti bakwai sannan na budeshi na zuba su maggi curry tumeric sena dan kara ruwan zafi na kuma rufeshi
- 2
Sannan na gyara albasa na yanyankata se nama shima na yanyankashi se attaruhu na jajjaga shi se zogale na taitstsinke shi na gyara na wanke
- 3
Sena dauko wnn kwanon da na zuba su couscous din sena zuba wnn attaruhun da albasa da nama na juya sosai sena zuba zogalena na jujjuya sosai na kara mishi mai
- 4
Sena dauko tukunyar dambu zan turarashi nazuba acikin kasa kuma na zuba ruwa a tukunyar kenan sena rufeshi ya turaru bayan minti ashirin yayi sena sauke na jiye a mazubi na saka mai da yaji
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai