Bredin kabewa meh rose

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#BAKEBREAD.Wannan bredin yana da dadi sosai musamman da farfesu,yana yanayi da alkubus saboda shima turarashi akeyi.

Bredin kabewa meh rose

#BAKEBREAD.Wannan bredin yana da dadi sosai musamman da farfesu,yana yanayi da alkubus saboda shima turarashi akeyi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 70 gKabewa bararre
  2. Hadin yeast:
  3. 3 gYeast
  4. 5 gSikari
  5. 45 gRuwan dumi
  6. Hadin flour:
  7. 190 gFlour
  8. 30 gSikari
  9. Baking powder 1/2 karamin chokali
  10. 15 gBota

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki wanke kabewan ki seh ki zuba a steamer ki turarashi har seh ya dahu,seh ki farfasa shi da chokali meh yatsu ya farfashe ki aje gefe.

  2. 2

    Seh ki samu kofi ki hada hadin. Yeast dinki a ciki ki zuba ruwan da yeast da sikari ki juya kibarshi tsawon minti 5 har seh ya kumburo.seh ki samu roba meh fadi ki tankade flour a ciki ki zuba sikari da baking powder seh ki zuba hadin yeast da butter da kabewan a ciki.

  3. 3

    Seh ki zuba sauran ruwan a ciki ki kwaba har seh ya hade jikinsa.ki shafa mai kadan cikin roban seh ki maida kwabin flour din ciki ki rufe da kling film ya tashi tsawon minti 45.

  4. 4

    Idan ya tashi seh ki kara kneading kwabin tsawon minti 3 ko 4,ki raba shi gida uku seh ki mulmula kowanne ki aje.seh ki dauki daya ki murzashi yayi tsawo seh ki raba gida biyar.Haka za kiyi da sauran.

  5. 5

    Seh ki dauki kowane hadin flour da kika raba gida biyar ki fadadashi ki aje gefe har seh kin fadada guda biyar.seh ki dakko daya ki aje ki sake dako wani ki daura akai haka zakiyi har ki jera guda biyar din kina dan danna shi kadan in kin daura kan daya.seh ki nadeshi a hankali kamar tabarma kina danna bakin ya hade har ki nade shi gaba daya seh ki dan murza shi bakin ya hade.

  6. 6

    Seh ki sa wuka ki yanka shi gida biyu daga tsakiya zeh baki siffar rose seh ki gyagyara yanda zeh baki ganyan rose din kina dan bubudesu da hannun ki.

  7. 7

    Seh ki samu parchment paper ki yankasu ki daura kowane rose akan guda daya.seh ki jera su cikin saman steamer ki samu kitchen cloth ki rufe saman ki barshi ya kara tashi na minti 30

  8. 8

    Bayan minti talatin seh ki cire kitchen cloth din ki rufe da murfin steamer din.seh ki zuba ruwa cikin kasan steamer din ki daura tukunyar saman meh bredin rose din.ki turarashi a high heat na minti 20 zuwa 25.seh ki kashe wutar ki dan bude murfin yadda turirin zeh rika fita tsawon minti 2 ko 3.saboda kar suyi shrinking.seh ki sauke,a ci lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

Similar Recipes