Miyan kubewa danya da ganye

Sophie's kitchen
Sophie's kitchen @sophiex
Kaduna

Ku gwada miyar nan Ku gani,zaku ji
dadin ta sosai.#kadunacookout

Miyan kubewa danya da ganye

Ku gwada miyar nan Ku gani,zaku ji
dadin ta sosai.#kadunacookout

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kubewa (yankaka ko kiyi grating)
  2. Nama (ko wane iri)
  3. Crayfish (dakakke)
  4. na kalwa (iru) Cokali 2
  5. Tarugu da tattasai (jajjage)
  6. Ganyen ugu ko alaiyahu
  7. Albasa
  8. Manja
  9. Dandano
  10. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A wanke nama,a tafasa shi a wuta da dandano,gishiri,da albasa har sai ya dahu.

  2. 2

    Dora tukunya a wuta,a sa manja,sai a sa yankaka albasa,a zuba kalwa ki,ki soya su sama sama,sai ki zuba kayan miyar ki ki soya.

  3. 3

    In ya soyu,sai ki zuba naman ki da ruwan tafashen,ba a cika ruwa da yawa,kisa crayfish,sai kisa dandano da gishiri yanda ake bukata.

  4. 4

    In ya tafarfasa sai ki rage wutar,ki zuba kubewar ki,ki motsa,sai ki Kawo ganyen ki kamar cikon hannu biyu ki zuba,da ya dahu kamar minti uku sai a sauke don kar ta dafe.

  5. 5

    Sai a zuba a ci da tuwo ko wane iri,ni dai nafi son ta da semo.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Sophie's kitchen
rannar
Kaduna
......no one is born a great cook,one learns by doing.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes