Milk-Crackers

Jahun's Delicacies
Jahun's Delicacies @4321ss
Kano,Danladi Nasidi Estate.

Nayi Spicy Crackers naji dadinsa, sai na gwada na madara sai na kasa banbance wanda yafi dadi a cikin su.

Read more
Edit recipe
See report
Share

Ingredients

  1. For the dough
  2. 1 cupFlour
  3. 2 tbspSugar
  4. 1/4 tspSalt
  5. 3 tbsppowdered Milk
  6. 1/2 tspmilk Flavor
  7. 1/2 tspOil
  8. 1/3 cupWater
  9. For the chocolate sauce
  10. 1 tbspCocoa powder
  11. 2 tbspSugar
  12. 2 tbsppowdered Milk
  13. 1/4 tspFlavor
  14. 1/4 cupWater
  15. Thickner(Flour Gel)
  16. 1 tspflour
  17. 1 tspwater

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki auna kofi daya na fulawa ki zuba a roba, ki saka siga da gishiri(ga awonsu na bayar a sama).

  2. 2

    Ki saka madarar gari, flavor na madara da ruwa(duk ga adadin da ake bukata a sama)sai ki kwaba.

  3. 3

    Ki barshi yai minti hudu zuwa biyar.

  4. 4

    Zaki gutsura ki murza yai fale fale(da injin taliya nayi) sai ki samu kofi(mai karamin baki) ki fitar da shape din,ki saka fork kiyi huda a jiki(air space).

  5. 5

    Ki dora mai yai zafi sai ki soya. Zaki ringa juyawa akai kai kar ya qone.

  6. 6

    Ga yanda ake so yayi.

  7. 7

    Ko a haka zakiji dadinsa, amma bari a kara masa dadi, da hadin chocolate sauce.

  8. 8

    Zaki samu roba karama ki zuba cocoa powder, madarar gari, siga ki juya, sai ki zuba ruwa da flavor ki dama, ki juye a tukunya ki kunna wuta ya tafasa. Sai ki auna fulawa karamin cokali daya ki zuba mata ruwa karamin cokali daya ki dama yai kauri, sai ki juye a cikin wanan hadin naki na kan wuta, nan da nan zakiga yayi kauri, sai ki saka mai ki juya ki sauke.(Duk na bada adadin da ake bukata a sama).

  9. 9

    Ga milk crackers ta hadu da chocolate sauce.

  10. 10

    Zaki dangwala kici. Dadi dai ba'a magana.

Reactions

Edit recipe
See report
Share

Comments

Written by

Jahun's Delicacies
on
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Read more

Similar Recipes