Kayan aiki

  1. Doya
  2. Mangyada
  3. Tattasai
  4. Tarugu
  5. Timatir
  6. Albasa
  7. Gishiri
  8. Seasonings

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki fire doyan ki,ki yayyan ka, Sai ki dauraye.

  2. 2

    Kisa mangyadan ki akan wuta,in yayi zafi,Sai ki barbada gishiri kadan a doyan ki, Sai ki ziba a mangyadan. Ki bari ya soyu, kaman yanda kike soya dankalin turawanki. Inya soyu Sai ki sauke.

  3. 3

    Sauce kuma, ki wanke Kayan miyan ki, Sai ki tube albasa a chikin su, Sai ki daddaka koh ki markada kayan miyan amman kada suyi laushi.

  4. 4

    Daga nan Sai ki ziba kayan miyan ki a saman wuta harsai ruwan ya dan tsotse, Sai kisa mai ki soya kahin ya soyu Sai ki yayyanka albasan ki yanda kikeso, Sai ki sa a sauce din, Sai ki sanya seasonings dinki dai dai yanda zayayi dadi.

  5. 5

    Daga nan, inya soyu Sai ki sauke.

  6. 6

    Daga nan kin gama kenan. Sai ki zauna kichi abinki chikin jin dadi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
wasila bashir
wasila bashir @cook_19441224
rannar
kaduna

sharhai

Similar Recipes