Hadin meatpie

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Wannan hadin yanada dadi kuma ba dole sai meat pie kadai zakiyi amfanidashiba zaki iya amfani dashi a semosa spring roll da sauransu #girkidayabishiyadaya

Hadin meatpie

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Wannan hadin yanada dadi kuma ba dole sai meat pie kadai zakiyi amfanidashiba zaki iya amfani dashi a semosa spring roll da sauransu #girkidayabishiyadaya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Dankalin turawa guda uku
  2. Albasa babba daya
  3. Attarugu
  4. Karas manya biyu
  5. Koren tattase babba daya
  6. 2 cupNikakken nama
  7. tafarnuwaCitta da
  8. Mai kadan
  9. Kurkur tsp daya
  10. Corn flour tspn daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fere dankalin kiyankata kanana sai ki ajiye agefe sannan kiwanke karas ki kankare bayan sai kiyankata kanana hakama koren tattase da albasa duk kiyankasu ki ajiye agefe

  2. 2

    Sai kidaura pan ko tukunya a wuta kisa mai kadan sai kixuba albasa kidan soyata sai ki jajjaga Citta da tafarnuwa kixuba akai kijujjuya sannan kidauko nikakken nama kixuba akai ki jujjuya har naman yacanza kala sannan kidauko dankali kixuba akai kicigaba da juyawa

  3. 3

    Bayannan sai kisa attarugu da karas kijujjuya sai kisa maggi curry thyme da sauran sinadaran dandano kijuya

  4. 4

    Sai kisa ruwa rabin kofi kijuyata sai kirufe kirage wuta kibarta nadan mintuna kadan don yashanye ruwan idan yashanye sai ki daama corn flour da dan ruwa kadan sai kixuba akai kijujjuya sai kibarta na minti daya zuwa biyu sai kisauke

  5. 5
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes