Kayan aiki

  1. 4Dankali hausa
  2. 1 cupFlour
  3. 2Egg
  4. 1Albasa
  5. 4Tarigu
  6. Maggi
  7. Salt
  8. Oil for frying

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaa wanke dankali hausa a dora a tukunya a dafashi da bawonshi kar a bari ya dafu yayi taushi sosai Sai sauke a kan wuta a bare bayan dankali a murmusa shi ko a daka shi

  2. 2

    Sai a daka tarigu da albasa a zuba Maggi da gishiri a cikin kayan miya sai a dauko dankali a zuba kayan miya a ciki a jujuya shi yanda zai hade

  3. 3

    Sai a zuba flour a cikin dankali yanda zai hade tunda shi dankali hausa yana da ruwa ruwa ba yanda zai hade va tare da ansa mai flour ba sai juya shi a mulmula shi

  4. 4

    Sai a fasa kwai a wani bowl daban a zuba gishiri kadan sai a zuba flour a wani bowl din daban ana saka dankali cikin egg din sai a saka dankali cikin flour sai a saka cikin mai ana soyawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes