Miyar ganye (vegetable soup)

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Inason miyar ganye musamman taji kayan hadi da ganyayyaki ga dadi ga kuma karin lafiya a jiki. 😋

Miyar ganye (vegetable soup)

Inason miyar ganye musamman taji kayan hadi da ganyayyaki ga dadi ga kuma karin lafiya a jiki. 😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tattasai,tarugu,albasa da tumatur kadan
  2. tafarnuwaChitta da
  3. Manja
  4. Nama da kashi
  5. Stock fish da ganda
  6. Daddawa
  7. Dandano
  8. Gishiri
  9. Cray fish
  10. Ganyen ugu
  11. Ganyen water leaf
  12. Alaiyaho
  13. Lawashin albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki wanke naman da kashi ki tafasa shi,shima ganda da stock fish ki wanke ki tafasa ki aje gefe.ki wanke ganyayyakin ki yanka ki aje gefe.

  2. 2

    Ki wanke kayan miyan ki saka chitta da tafarnuwa ki nika amma kar yayi laushi kamar jajjage.seh ki dora tukunya kan wuta ki zuba manja ki yanka albasa kadan ki zuba.idan albasar ta dan soyu seh ki zuba kayan miyan.idan ta fara soyuwa seh ki zuba daddawa ki juya.

  3. 3

    Ki zuba dandano ki juya ki barshi ya soyu,idan mai ya fara fitowa seh ki zuba nama da stock fish da ganda ki zuba ruwan naman,seh ki zuba cray fish ki juya ki barshi ruwan ya dan janye miyar tayi kauri.

  4. 4

    Idan miyar tayi kauri ta soyu seh ki zuba lawashi ki barshi kaman minti 3 sannan ki zuba ugu shima yayi kamar minti 3 seh ki zuba water leaf ki juya ki barshi yayi kamar minti 2 sannan ki zuba alaiyaho ki juya idan da bukatar karin dandano ko gishiri seh ki kara ki barshi ruwan ya dan janye kamar minti 4 seh ki sauke. Ana iya ci da tuwo,semo,sakwara,shinkafa da sauransu.sannan kina iya sa duk naman da kike so kamar su kayan ciki da busashen kifi.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes