Hadin shinkafa mai kayan lambu

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Sha shida ga watan maris din wannan shekara da muke ciki nayi tafiya izuwa jihar kaduna(zaria)ranar ya kasance na kai azumi ina kwadayin cin shinkafa da taji hadi sosai,dama mun je ne don kai mahaifiyata ziyartar likita,mun je asibitin a hanya sai na tsaya na siyi kayan lambun da nk so(na taho da wasu daga kano)amma na rasa koren tattasai😏(yan zaria🙄).......na dawo gda dai na shirya shinkafata naci,naji dadinta sosai hk sauran yan gdan.To tunda na baro zaria shinkafa ta min qabe qabe a zuciya kawai so nk in qara cin irinta,ai ko banyi qasa a gwiwa ba na harhada kan kayan lambuna na qara maimaitawa,sai dai wannan akwai yan qare qare a cikinta da kuma ragin abinda ba a rasa ba itama naji dadinta sosai(dama in dai shinkafa ce ko a yaya tazo zamu ci cikin nishadi😁😂)wancan na farko bani da hotonshi daki daki shi yasa ban saka ba,amma ga bashi nn na biya😊a cigaba da girki cikin nishadi da walwala🤗👩‍🍳✌

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1 da min 30m
4 yawan abinchi
  1. Kofi uku na shinkafa(wadda ta dauko dahuwa bata qarasa ba)
  2. 100 gbutter
  3. Nau'in naman da ake so
  4. Kofi daya na karas(yankakke)
  5. Kofi daya na koren wake(yankakke)
  6. Rabin kofi na yankakken koren tattasai
  7. 3/4kofi na cauliflower
  8. Albasa yankakkiya(yadda ake son yawanta)
  9. Cikin hannu na yankakken parsley
  10. Sinadarin dandano
  11. Kayan qamshi,tafarnuwa,curry da garin yaji

Umarnin dafa abinci

hr 1 da min 30m
  1. 1

    Da farko za a narka butter a cikin tukunya,sai a zuba tafarnuwa a dan soya kadan sai a zuba yankakken naman da ake amfani dashi,sai a zuba albasa albasa a juya,a soya na minti biyu

  2. 2

    A kawo dan gyadar qamshi da thyme a zuba a qara juyawa sai a zuba karas a qara soyawa sama sama,sinadarin dandano ya biyo baya

  3. 3

    Sai a zuba koren wake da cauliflower a juya na minti daya,kayan qamshi ya biyo baya(hadi na musamman😉)

  4. 4

    A zuba curry da garin yaji a qara soyawa na lkc kadan,sai a kawo ruwa dan daidai yadda zai qarasa dafa shinkafar a zuba

  5. 5

    Sai a zuba shinkafar a cakude a sai a zuba ganyen parsley din a sama a rufe da kyau a barshi ya dan fara tirara,sai a zuba yankakkiyar albasa daga sama a qara rufewa ta qarasa

  6. 6

    In tayi shinkafar sai a zuba koren tattasai a cakude....aci dadi lafiya,naci wnn shinkafar da girgijen madara mai dadi da sanyi,a gwada yan uwa aji dadi😚❤(hoton qarshe na shinkafar da aka kwaikwaya ne)

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes