Dambun Acca

Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
Sokoto

Wannan girkin nayishi musamman ga diabetic patient

Dambun Acca

Wannan girkin nayishi musamman ga diabetic patient

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2 hr
2 yawan abinchi
  1. Kofi 2 na acca
  2. Tattasai 5 manya
  3. 8Tarugu
  4. 2Albasa manya
  5. Mai 1/2 kofi
  6. 4Kifi soyayye manya
  7. 30Alayyahu na
  8. 3Tafarnuwa
  9. 1Citta
  10. Curry
  11. Dandano(magi) kalolin da kike so

Umarnin dafa abinci

2 hr
  1. 1

    Zaki fara wanke acca dinki,sai ki raigayeta,sbd tsakuwa.

  2. 2

    Sai ki jikata na tsawon minti 10

  3. 3

    Sai kixo kiyi grating tattasai,taruga da albasa 1.

  4. 4

    Dayan albasar kuma sai ki yayyankata ki ajiye a gefe.

  5. 5

    Ki yanka alayyahu ki wanke ki aje shima agefe

  6. 6

    Sai ki daka cittarki da tafarnuwa suma.

  7. 7

    Ki dauko kifinki ki cire masa kaya ki ajiye gefe.

  8. 8

    Ki koma ga accarki ki tsiyaye mata ruwa kisa akwando ta tsane ruwa.

  9. 9

    Sai ki saka ta a madambaci ki turara ta na tsawon minti 30.

  10. 10

    Idan tayi sai ki sauke ki kwashe a roba mai fadi,ki bari tasa iska.

  11. 11

    Sai ki saka cittarki da tafarnuwa da kika daka,sai ki saka curry,da magi,k motse su hade jikinta.

  12. 12

    Ki saka kayan miyar ki da Alayyahu ki gauraya sosai,sai ki saka mai.daga karshe sai ki saka kifinki da Albasa da kika yanka.

  13. 13

    Ki gauraya komi y hade sosai..

  14. 14

    Sai ki maida a madambaci y turara na tsawon minti 20.

  15. 15

    Sai ki sauke.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
rannar
Sokoto
cooking is my passion
Kara karantawa

Similar Recipes