Bhindi masala(miyar kubewa)

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan miya shahararriyar miya ce a qasar hindu,mafi buqatuwar kayan amfaninta su ne:kubewa,albasa,tumaturi sai kayan qamshi(spices♨️)an fi cin shi da roti(burodi)samfurin....amma ni na ci tawa da shinkafa ne qasar,yana da dadi sosai...ni da mahaifiyata mun ji dadinshi😋amma yar uwata kamar ta zaneni🤣wai abinci ga dandano har dandano ga qamshi amma na zubawa kayan yauqi😏

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

min 20mintuna
5 yawan abinchi
  1. 300 gkubewa
  2. Albasa babba biyu
  3. Tumaturi hudu
  4. Nama(za6i)
  5. Shambo guda hudu
  6. Attaruhu hudu
  7. Bay leaves
  8. 1/2qaramin cokali na curry
  9. 1/2qaramin cokali classic mix
  10. 1qaramin cokali na tandoori masala
  11. 1qaramin cokali na garam masala
  12. 1/2qaramin cokali na biryani masala
  13. 1/2qaramin cokali na bbq mix
  14. Sinadarin dandano (yadda zai isa)
  15. Mai Kofi daya

Umarnin dafa abinci

min 20mintuna
  1. 1

    Wadannan su ne kayan da nayi amfani da su,duk na yayyankasu ne a tsaye

  2. 2

    Da farko za a fara da zuba mai cikin tukunya,idan ya yi dumi sai a zuba yankakkiyar ku6ewar,ana soyawa hade da juyawa lokaci daya na tsahon minti biyar,zai fara laushi,sai a hada duka kayan qamshin a zubasu a juya sai a zuba albasa

  3. 3

    A soya na minti biyu,sai a kawo yankakken nama da aka tafasa,attaruhu da bay leaves a zuba,minti daya sai a zuba shambo(za a iya saka guda guda ko a yanka gida biyu) a zuba maggi a juya

  4. 4

    A dan barbada gishiri kadan,a bashi minti daya sai a kawo yankakken tumaturi a zuba a juya...a rage wuta can qasa,bayan minti daya a kashe wutar...miyar tana da dadi sosai wlh.

  5. 5
  6. 6
Gyara girkin
See report
Tura

sharhai (12)

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Will you mind been my urdu teacher??pls

Wanda aka rubuta daga

Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes

More Recommended Recipes