Miyar busheshen karkashe

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Busheshen karkashe
  2. Gyada
  3. maggi
  4. Nama
  5. albasa
  6. gishiri
  7. toka/ da kanwa dai baza tayi kyau b
  8. tafarnuwa
  9. citta
  10. tattasai
  11. attarugu
  12. man gyada
  13. daddawa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko dai zaki dafa nama da gishiri tafarnuwa citta albasa, sai naman ta dahu tanuna tayi laushi, sai ki zuba mai dan daidai ki soya naman ya suyo, kisa daddawa ki soya su tare.

  2. 2

    Sai kisa ruwa daidai yawan da kikeso, kisa maggi sai ki gusura gyada ki murzata cikin ruwan miyar ba tare da kin damata da ruwa ba.

  3. 3

    Sai ki debo toka kadan bamai yawa ba ki zuba sai ki rufe amma fa kar kiyi nisa da tukunyar dan inta fara tafasa zubewa za tayi

  4. 4

    Zaki barta ta dan dahu don gyadar tanuna. Sai ki gyara karkashen ki, ki murzata ki cire dattin duka sai ki bakace ta duk kasan zai fita

  5. 5

    Sai ki duba ruwan miyar in tayi daidai, sai ki kada ta, amma fa kar kisata dayawa dan tana kumbura, ba kamar danyenta ba

  6. 6

    Nan ne zaki saka jajjagen tattasai da attarugu sai ki rufe ya dahu yanuna yayi yauqi. Kalas

  7. 7

    Kina kuma iya yinta da wake amma ita sai kin dafa waken ta nuna sai ki kadata. Kuma yana son daddawa 🤣

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Aisha Ardo
Aisha Ardo @cook_26614272
rannar
Abuja Nigeria

sharhai

Similar Recipes