Kayan aiki

  1. Alkama mudu daya
  2. Sugar gwangwani 6
  3. Nonon shanu
  4. Butter simas rabi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki sheqe alkaman ki a cire daukkan dattin ko a wanke a baza shi a rana ya bushe

  2. 2

    Sai a kai niji a mishi barjin fate idan ake dawo dashi a bude tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a juye nonon shanu, butter sai a murje shi da kyau y hade.

  3. 3

    Sai zuba ruwa amma kwabin da zaki masa mai qarfin gaske yanda zai hade da kyar

  4. 4

    Sai a rufe shi y kwana

  5. 5

    Idan kika tashi da safe sai ki jiqa kanwa ki rinqa yayyafa masa kina hadeshi kina bugawa.

  6. 6

    Sai ki diba da hannun ki kina masa nad'in alkaki kin ga bai karye ba. Wato kin yi tsaho dashi kin murza duka bai karye ba. Kin ga ba qaramin bugu zaki masa ba. Ba'a jibga masa ruwa yayyafa masa zaki rinqa yi kina buga shi.

  7. 7

    Sai a zuba sugar a tukunya a zuba ruwa kamar kofi uku a daura a wuta sai ki saka lemun tsami yayin dafawa

  8. 8

    Wurin dafa sugara a kula yana fara yin kumfar farko na dahuwa a d'iba a cokali Yana dan fara shan iska zaki ga yayi danqo

  9. 9

    Sai a sauke don haka kada ki barshi yayi ta dahuwa.

  10. 10

    Wuri soya alkakin ki daura mai a wuta sai ki saka wutan kadan kadan yadda cikin zai soyu

  11. 11

    Bayan y soyu kin kwashe sai ki saka a cikin sugar sai ki kwashe na cikin sugar kina sawa a kwano.

  12. 12

    Shikenan enjoy 😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jidda Kitchen
Jidda Kitchen @Chef_jidda
rannar

Similar Recipes