Kwakumeti

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Ga #kwakwa na cikin lokachin ta kuma tana da arha ina ta tuna nin me zanyi a wannan kalubalen se kawai kwakumeti yazo min arai gashi nayi kadan kuma yayi dadi😅

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

Awa 1mintuna
1 yawan abinchi
  1. 1Kwakwa da aka goga kofi
  2. Rabin kofi na suga ko kasa da haka
  3. Bota Ko Mai chokali 1

Umarnin dafa abinci

Awa 1mintuna
  1. 1

    Zaki fasa kwakwa ki yanka ta

  2. 2

    Sannan ki wanke ta tass

  3. 3

    Kisa magogi(grater) ki goga manya yafi kyau

  4. 4

    Se ki auna kofi 1

  5. 5

    Se ki zuba rabi kofi n suga ciki sannan ki motsa

  6. 6

    Ki zuba mai ko buta cikin frying pan yayi zafi amma ba sosai ba

  7. 7

    Se ki zuba kwakwar da kika sa ma suga kiyi ta motsawa

  8. 8

    Baa barin motsawa kada ya kone yayi dachi kisa wuta kadan

  9. 9

    Idan min kashe kada ki bar motsawa zata hade kiyi ta motsawa har ta huche

  10. 10

    Se ki samu mazubi me aminchi ki zuba ki rufe

  11. 11

    Mukam ba wani rufewa yau zamu chinye 🤣

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes