Brodin HABBA da RIDI me Kitso

Ummi Tee
Ummi Tee @Ummitunau
Sokoto

#BAKEBREAD yarana son biredi, shi ya kara harzikani in iya domin jin dadinsu, musamman idan na samishi ridi da habbatu sauda domin qarin lafia ita habba ta na magani da yawa ga jikin yara kuma ridi na qara basira.

Brodin HABBA da RIDI me Kitso

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#BAKEBREAD yarana son biredi, shi ya kara harzikani in iya domin jin dadinsu, musamman idan na samishi ridi da habbatu sauda domin qarin lafia ita habba ta na magani da yawa ga jikin yara kuma ridi na qara basira.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kohi 2 na filawa
  2. Chokalin cin abinchi 2 na suga
  3. Karamin Chokali na gishiri
  4. Kwai daya
  5. Yis chokali biyu
  6. Bota chokali 3
  7. Ruwa rabin kohi
  8. Habbatusauda
  9. Ridi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Bi daki daki da yadda zaka hada kayan hadin burodi yanada anfani matuka. Hanyar datafi sauki wurin hadin biredi shine ka hada da hannu idan kuma kanaso kana iya yi da chokali idan yafara tauri seka cigaba da hannu

  2. 2

    Zaki dauko yis dinki ki zuba cikin ruwanki masu dumi. Se ki tankade duk busassun kayan hadinki wato filawa gishiri da sauranki acikin kwano me wali me dimi

  3. 3

    Seki zuba botarki cikin filawa ki yamutse se kiyi dan rame a tsakiyar filawarki ki zuba ruwan yis dinki

  4. 4

    Se kisa hannu ki hade ruwan tare da filawarki kina hadawa a hankali dan komai yasamu ya hade tare ki murza da hannu yabi jiki ya dunkule. ki murza samasama cikin kwanon.

  5. 5

    Murza hadinki na biredi abune da baki iya tsallakewa ko bari idan baza ki iya murza hadinki da hannu ba to kina iya anfani da food processor wato injimin hadawa. Murza hadi shi kesa hadinki yayi dimi ya kuma yi laudi. Laudin ganinki gami da yis shi kesa biredi yayi sakwai yayi saka a ciki. Rashin murza hadi zesa biredi yayi tauri kuma bazeyi saka ba idan kinsa a abun gashi seya fada ciki.

  6. 6

    Yadda ake murzawa. Zaki barbada filawa saman wuri me tsafta se ki dauko hadinki ki aza a wurin ki barbade hannunki da filawa zaki yita murza hadinki kinaja kina turawa baya kina dawo dashi gaba ya zamana de ko ina an murza shi har tsawon minti goma.

  7. 7

    Se ki dauko hadinki kisa cikin kwanonki wanda kika bishi da bota ana yin hakane saboda kada hadin ya lake a Kwanon. Ledar daki rufe kwanon itama kishafa mata bota dan kada saman hadin ya bushe

  8. 8

    Ki samu wuri me dumi ki aje kwanonki na tsawon awa daya da rabi ko biyu nan zakiga hadinki ya ninka hadin farko sau biyu

  9. 9

    Idan hadinki yayi biyun farko se ki kara murzawa na tsawon minti daya zuwa biyu yin hakan zesa iskan dake cikin hadinki ya baje ko ina ya samu iska

  10. 10

    Se ki raba hadinki kashi ukku kashin su zama daidai da juna seki mulmula kashin kamar kwallo sannan ki mulmula shi yayi tsawo

  11. 11

    Seki kitsa hadinki saman kwanon gashi idan kinkai karshe seki game bakunan ki tura karkashi. Ki dauko leda me mai ki rufe ki barshi ya kara tashi na tsawon minti talatin zuwa awa daya

  12. 12

    Idan hadinki ya kara tashi se kisamu broshi ki shafa kwai sama ki barbada habbatusauda da ridi

  13. 13

    Se kisa cikin abun gashi wato obun dinki ki gasa biredinki na tsawon minti talatin

  14. 14

    Yadda zaki gane ya gasu zaki chiroshi ki kwankwasa bayanshi idan kinji yayi kara me kamar ba komai a ciki to ya gasu

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummi Tee
Ummi Tee @Ummitunau
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes