Nad'add'en biredi mai nutella a cikinsa

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa kofi biyu
  2. Suga cokali uku
  3. Yis cokalin shayi daya
  4. Bota cokali daya
  5. Kwai guda daya
  6. Madara cokali daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki zuba ruwa mai gumi a cikin yis, sai ki juye a roba mai girma. Ki zuba kwai, madara, bota da suga ki motse sosai har sai komai ya narke.

  2. 2

    Ki zuba filawar a ciki ki motse sannan ki jiya a cikin wancan kwa6in. Ki murza sosai.

  3. 3

    Ki saka a leda sannan ki sa a ciki firij ya yi sanyi sannan ki fiddo.

  4. 4

    Ki baza shi ya yi fadi sai ki nemi wani abu zagayayye ki fidda. Ki nemi cokali ko karamar wuka ki shafe shi duka da nitella. Sai ki fara nadewa kamar kina nade tabarma.

  5. 5

    Ki shafe shi da kwai sannan ki Saka a na'udar gasawa ki gasa har sai ya yi kalar zinari. Sai ki fitar. A ci da shayi ko lemu

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes