Zagayayyar filawa mai nama (meat pie)

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

Zagayayyar filawa mai nama (meat pie)

Masu dafa abinci 6 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa kofi biyu
  2. Bota cokali daya
  3. Bekin hoda rabin cokalin shayi
  4. Kori rabin cokalin shayi
  5. Nama
  6. Kayan kamshi
  7. Albasa rabi
  8. Kwai 1 (saboda shafawa)
  9. 1Karas

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki hade busassun kayan hadi a wuri guda ki motse. Sai ki zuba bota ki sake motsawa. Ki zuba ruwa kadan ki buga.

  2. 2

    Ki nika nama ki zuba a cikin kasko, ki zuba albasa da kayan kamshi sai dandano. Ki hau motsawa.

  3. 3

    Ki dama filawa kadan ki zuba a ciki da karas gurzajje. Idan ya yi sai ki sauke.

  4. 4

    Ki nemi irin abun fitarwa ana siyar da shi a kasuwa. Sai ki baza filawar ta yi fadi sannan ki yanka daidai girman abun. Ki dora a kai ki zuba kayan hadin cikin sannan ki matse. Za ki ga ya hade. Sai ki cire. Haka zakiyi har ki gama.

  5. 5

    Sai ki fasa kwai ki fitar da kwaiduwar. Ki nemi buroshi kina shafewa da shi kamar haka

  6. 6

    Sai ki saka a naurar gashi ki gasa har sai ya yi kalar gwaldin

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes