Grilled chicken

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#kaduna2807.Gashin kazan nan na da dadi sosai musamman idan kayi marinating over night sinadaran da ka hada na marinade fin sun fi ratsa kazar a hankali ga dandano meh dadi.

Grilled chicken

Masu dafa abinci 11 suna shirin yin wannan

#kaduna2807.Gashin kazan nan na da dadi sosai musamman idan kayi marinating over night sinadaran da ka hada na marinade fin sun fi ratsa kazar a hankali ga dandano meh dadi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Kazar agric guda
  2. 5Dankali kamar guda
  3. 1Carrot babba guda
  4. Jajjagen tattasai,tarugu,da albasa
  5. Dandano
  6. Kayan kanshi
  7. Bota
  8. Mayyonaise
  9. Soysauce

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki wanke kazarki ta tsane tas seh ki hada jajjagenki yadda kike bukata da mayyonaise,dandano,spices,soysauce.Seh ki shafe kazarki ko ina ya ji bayan kin tsaga wurin tsokar dan hadin ya ratsata.kafin nan ki dibi hadin kadan ki aje saboda shafawa a jikin kazar yayin gashi kuma ki dan hada cikin dankalin.seh ki samu leda ki sata ki rufe ki sa a roba ki sa a fridge ta kwana.

  2. 2

    Kafin ki fara gashin,ki fere dankalin ki ki dafa shi amma kar ya dahu duka seh ki tsane.ki yanka carrot da albasa kadan ki hada da dankalin seh ki zuba hadin marinade din da kika aje kadan a ciki ki juya.ki dakko kazar ki seh ki shafa mata bota a karkashin fatar seh ki zuba dankalin a cikin ta seh ki tura kafafun ta kasan gurin zunbutun kar hadin da kika zuba ya zubo.seh ki sa a abun gashi.Nayi amfani da halogen oven.

  3. 3

    Idan tayi kamar minti 30 seh ki kara shafa mata hadin ki juya kasan ki kara maida ta kinayi kina dubata har ta gasu.A chi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes