Sauce din naman akwiya

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Inason naman akwiya yana da dadi sosai ga kamshi da dandano na daban.

Sauce din naman akwiya

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Inason naman akwiya yana da dadi sosai ga kamshi da dandano na daban.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Naman akwiya
  2. Albasa (jajjage)
  3. Kayan miya (jajjagen tarugu,tattasai,shambo)
  4. Kori
  5. Dandano
  6. Kayan kanshi
  7. Gishiri
  8. Jajjagen tafarnuwa da citta
  9. Mai
  10. Bay leaf
  11. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki wanke namanki sai ki zuba a tukunya kisa dandano,albasa,bay leaf,citta da tafarnuwa da kayan kanshi.sai ki sa gishiri kadan da ruwa kadan ki dora a wuta ki tafasa.

  2. 2

    Bayan ya tafasa sai ki dora mai ki soya shi sama sama.

  3. 3

    Ki samu tukunya ki dora ki zuba mai dai dai misali,idan yai zafi sai ki zuba albasarki ki dan soyata sai ki zuba citta da tafarnuwa ki barshi ya dan soyu kadan.sai ki zuba kayan miyan ki kisoya.

  4. 4

    Idsn ya dan soyu sai ki zuba ruwan naman ki ki sa dandano da kori ki kara kayan kanshi da gishiri sai ki kawo soyayyen namanki ki zuba ki rufe ya dan sulala.za a iya ci da soyayyen dankali da kwai ko doya,shinkafa ko duk abin da kike so.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes