Pepper chicken

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

Wannan harin kazar yayi matukar dadi,kuma iyalina sunji dadinta sosai tareda yabawa

Pepper chicken

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Wannan harin kazar yayi matukar dadi,kuma iyalina sunji dadinta sosai tareda yabawa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

biyu da rabi
8 yawan abinchi
  1. Kaza hudu
  2. 12Maggi
  3. 1Maggi fari
  4. Gishiri dan dandano
  5. 2Tarugu
  6. Albasa 1,babba
  7. Ma'ukhal(vinegar)
  8. Soyawa
  9. Mai,iya yanda zai isa
  10. Pepper
  11. Tarugu da tattasai,markadayye
  12. Mai,kadan
  13. Maggi
  14. Gishiri, kadan
  15. Curry
  16. Kayan kamshi
  17. Albasa da lawashi
  18. Albasa,kiyanka slice

Umarnin dafa abinci

biyu da rabi
  1. 1

    Da farko zaki zuba ruwan vinegar kadan acikin ruwan da zaki wanke kazar,saiki wankesu da kyau. Zakisa cikin tukunya batareda kin zuba ruwaba,ruwan jikinta da kika wanketa ya isa ya dafata(ammafa kazar turawa),saiki saka maggi da kuma gishiri

  2. 2

    Zaki yanka albasa da dan dama,da kuma tarugu ki zuba aciki. Amfanin saka tarugu aciki yana kara kamshi koda bakida kayan kamshin da zaki saka aciki,kuma yana cire karnin da kaza takeyi

  3. 3

    Ki rufe tukunyar kibarshi kamar mintuna shabiyar ta dahu,saiki kwashe ki aje gefe

  4. 4

    Zaki aza mai yayi zafi,saiki dauko kazan kisaka aciki kisoya,kada kibarta tasoyu sosai,saiki kwashe

  5. 5

    Acikin frying pan din da kikayi suya,zaki bar mai kadan saiki zuba nikakken tarugu da tattasai aciki,zaki barsu suyita dahuwa har sai ruwan sun kare kaziga ya fara soyuwa,saiki rage wuta,kinayi kina motsawa harsu soyu. Saiki zuba maggi, curry,kayan kamshi, gishiri kadan da kuma albasa da lawashi

  6. 6

    Ki motsa,sai kintabbata dukkanin kayan kamshin sun hade baki daya, sannan saiki saka albasa da kika yanka kuma

  7. 7

    Bayan ta soyu sama sama,saiki raba gida biyu kibar sauran cikin frying pan din

  8. 8

    Sannan saiki dauko kazar da kika dafa kisa aciki,ki koma zuba rabin da kika rage asama,hakan zaisa ko ina yagame da kazar

  9. 9

    Masha Allah,shikenan tayi 💃💃💃saici

  10. 10

    Yummy 😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

sharhai

Similar Recipes