Sakwara da miyar agushi

Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
Sokoto

Soyayyata da doya ba ze misaltu ba ba na gajiya da sarrafata

Sakwara da miyar agushi

Soyayyata da doya ba ze misaltu ba ba na gajiya da sarrafata

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Doya
  2. 1Agushi kofi
  3. Ganyen alayyahu
  4. 2Tattasai
  5. 3Tarugu
  6. 1Albasa
  7. Dandano
  8. Manja cokali3
  9. Soyayyen nama
  10. Daddawa cokali1

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki fere doya ki yanka ta ki wanke ki dafa har se tayi luguf

  2. 2

    Ki saka ta a turmi ki kirba ta har se tayi laudi ya zama ba kolallai se ki kwashe ki mulmula a saka a leda

  3. 3

    Ki yanka kayan miya kiyi blending ki yanka alayyahu ki wanke kisa a kwando

  4. 4

    Ki dora tukunya a wuta ki zuba manja ki yanka albasa in ya soyu ki zuba kayan miya ki bari su soyu

  5. 5

    Ki zuba agushi kiyita juyawa har su soyu se ki tsaida ruwan miya ki saka dandano da daddawa da alayyahu ki watsa soyayyen nama ki barsu su dahu

  6. 6

    Aci dadi lafiya

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
rannar
Sokoto
I love cooking though I'm not perfect but trying to be
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes