Fankek na aya

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#Sahurracipecontest# Ganin yadda abubuwan fulawa sukayi yawa,na kirkiro wani sabon hanyar sarrafa aya,ta hanyar yin fankek,kowa yasan amfanin aya da ingancinsa ajikin mu,kuma wannan fankek din yayi dadi sosai,fiye da zato na,iyalina sun yaba kuma sunyi santi.Kasancewar bana iya SAHUR da abinci mai nauyi ya sanya ni yin wannan lafiyayyar fankek.Had'i da shayi mai inganci da lafiya,Wanda aka had'a da itatuwa masu kamshi da inganci.

Fankek na aya

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#Sahurracipecontest# Ganin yadda abubuwan fulawa sukayi yawa,na kirkiro wani sabon hanyar sarrafa aya,ta hanyar yin fankek,kowa yasan amfanin aya da ingancinsa ajikin mu,kuma wannan fankek din yayi dadi sosai,fiye da zato na,iyalina sun yaba kuma sunyi santi.Kasancewar bana iya SAHUR da abinci mai nauyi ya sanya ni yin wannan lafiyayyar fankek.Had'i da shayi mai inganci da lafiya,Wanda aka had'a da itatuwa masu kamshi da inganci.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
3 servings
  1. 2Aya gwangwani
  2. gwangwani Sikari rabin
  3. cokali Bakar hoda karamin
  4. Kwai guda biyu
  5. Gishiri Dan kadan
  6. Mangyada
  7. Madarar gari cokali biyu

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    Ga kayan had'in mu

  2. 2

    Da farko na wanke ayar,na soya sama-sama,sannan na sheke tas,na nika ya zama gari

  3. 3

    Ban na nika,sai na tankad'e,sannan na zu sikari,bakar hoda,madarar gari,da dan gishiri Kazan

  4. 4

    Sai na kad'a kwai na zuba akai

  5. 5

    Sannan na jujjuya suka had'e kamar haka

  6. 6

    Sannan na d'ora kasko a wuta,na sanya mai kadan na soya,da dayan barayin yayi,na kifa,gashi kamar haka

  7. 7

    Ga sakamakon dana samu.Aci lafiya

  8. 8

    Na shayin(tea)kayan had'i,sune,abarba,citta,kanunfari,girfa,na'a na'a,ganyen zobo,lemon grass.dabino,mazarkwaila.ga kayan hadin,sauran an nikasu,shine a leda

  9. 9

    Na hadesu a tukunya,na dibi garin kayan kamshin karamin cokali,ga shi na zuba

  10. 10

    Na barsu,suka tafasa sosai

  11. 11

    Sannan na tace..Na sha da dumi

  12. 12

    Ga sakamakon.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes