Dubulan

Mamu
Mamu @1981m
Lagos

#Dubulan. Wannan girki anfiyinshi lokacin biki ko kuma a masarauta don karramawa, haka zalika nayima maigidanashi don karramawa kuma ya yaba.

Dubulan

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#Dubulan. Wannan girki anfiyinshi lokacin biki ko kuma a masarauta don karramawa, haka zalika nayima maigidanashi don karramawa kuma ya yaba.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kofi biyu na fulawa
  2. Madaran gari rabin kofi
  3. Baking powder Rabin cokali karami
  4. Bota babban cokali guda hudu
  5. Gishiri Dan kadan
  6. Mangyada na tuya da dan dama
  7. Sugar Kofi daya da lemun tsami daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Atanaji kayan aiki kamar haka fulawa, bota, baking powder, gishiri da madara, na hadasu wuri daya na cakude, idan na murza yana haduwa wuri daya, alamar cewa komi ya hadu kenan

  2. 2

    Nasamu ruwa masu dumi naxuba, nayita murzawa har yazama (dough) watau yayi karfi karfi laushi laushi, daidai yadda zakaji dadin aiki, da yayi na yanyanka kanana, kowanne daya nasa abun murzawa na fadadashi kamar a hoton kasa

  3. 3

    Nasamu abun yanka na yankashi ta tsaye tsaye, Sannan na dunkuleshi ta gefe, sannan na murzashi ya koma tsaye

  4. 4

    Sannan na dunkulashi taciki kamar wata tsutsa mai dunkulewa, sai kuma na mayardashi kamar fulawa

  5. 5

    Haka nayitayi harna gama, nasa mai a wuta, dayayi zafi nazuba dubulan aciki nasoya

  6. 6

    Daya soyu na kwashe, nadora wata tukunya a wuta, nasa ruwa da suga na matsa lemun tsami aciki dayayi kauri na sauke, na dauko dubulan ina tsomawa aciki ina shafe jikinshi da sugan harna kare.k

  7. 7

    Dubulan ya kamkama, ana iya cinsa da lemu. Nagode

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mamu
Mamu @1981m
rannar
Lagos
Eating is necessity but cooking is an Art, i just love cooking
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes