Red velvet cake

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Ina matukar son RVC.kalar shi ma kadai ya isa daukan ido.

Red velvet cake

Ina matukar son RVC.kalar shi ma kadai ya isa daukan ido.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 90 gButter
  2. 150 gSugar
  3. 2Kwai
  4. Buttermilk 3/4 kofi(ko ki hada,madara 3/4 kofi+1tbsp vinegar)
  5. Mai(Vegetable)3/4 kofi
  6. Vanilla karamin cokali 1
  7. 240 gCake flour
  8. Cocoa powder babban cokali 2
  9. Baking soda 3/4 karamin cokali
  10. Baking powder karamin cokali 1
  11. cokaliGishiri rabin karamin
  12. Food colour ja 1/2 karamin cokali ko yadda ake son jan sa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki hada duk kayan da kike bukata wuri guda. Sai ki hada dry ingredients dinki wuri guda ki tankade su cikin roba.

  2. 2

    Ki samu wani roban kuma seh ki hada butter da sugar kiyi mixing har ya hade yayi fari seh ki saka kwanki daya bayan daya ki na mixing duk sanda kika sa kafin kisa dayan.sannan ki sa mai,vanilla da buttermilk.Idan baki da buttermilk seh ki hada madaran da vinegar cokali daya ki juya ki barshi kamar minti 10 ko 15 seh kiyi amfani da shi.

  3. 3

    Seh ki zuba hadin flour dinki kadan kadan kiyi mixing har ya hade.sannan ki sa jan kalar ki kadan har yayi jan da kike so.seh ki zuba cikin gwangwanin ki da kika shafe shi da butter kika yi dusting da flour ki gasa a oven da kika riga kikayi preheating zuwa kamar minti 30 ko idan kika sa tsinken sakace kika ga ya fito ba alamar kwabin.seh ki cire ki barshi ya dan sha iska na minti 10 cikin gwangwanin sannan ki cire ki barshi ya huce sosai kafin ki sa icing din da kike so.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes