Soyayyen dankalin Hausa da egg sauce

karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
Kano

Soyayyen dankalin Hausa da egg sauce

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1:10mins
2 yawan abinchi
  1. Dankalin hausa
  2. Kwai hudu
  3. Timatir manya guda biyar
  4. Albasa karama
  5. Man gyada
  6. Maggi guda uku
  7. Gishiri
  8. Curry da thyme
  9. cokaliGinger and garlic pastes karamin
  10. Tarugu manya guda biyar

Umarnin dafa abinci

1:10mins
  1. 1

    Zaa fere dankalin a yanka shi a tsaye a sa ruwa sabida kada yayi baqi sai a dauraye shi asa masa gishiri kadan a gauraya a dora mai a pan babba in yayi zafi a zuba dankalin a soya shi sai yayi yanda akeson kalarsa sai a tsame shi a colander a bar shi ya tsiyaye.

  2. 2

    Zaa wanke timatir a yayyanka su a jajjaga tarugu a yanka albasa. A dora pan ko tukunya a zuba mai kadan sai a soya albasa sama sama sai a zuba garlic and ginger pastes din a jujjuya a zuba timatir a juya a barshi sai ruwan ya tsotse.sai a sa gishiri kadan asa maggi,curry da thyme in ya soyu sai a zuba kwai da aka riga a ka kada. A rage wutan kada a yi saurin juyawa.sai bayan kaman minti daya sai a juya. A ci gaba da juyawa sai kwan ya nuna sai a ci da soyyayyen dankalin.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes