Fura

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#FPPC fura wani nauin abinci neh da akeyi da gero da kayan kanshi,Ana dama shi da nono a Sha.Ina son fura sosai shiyasa nace Bari na gwada yinshi saboda yawanci Wanda zaka siya wani zaka ji kana Jin kasa,Amma idan kayi a gida yafi tsafta saboda zaka rege geron ka da kyau ka tsaftace shi.Na gwada Kuma yayi kyau yayi Dadi ga gardi ga kanshi.

Fura

#FPPC fura wani nauin abinci neh da akeyi da gero da kayan kanshi,Ana dama shi da nono a Sha.Ina son fura sosai shiyasa nace Bari na gwada yinshi saboda yawanci Wanda zaka siya wani zaka ji kana Jin kasa,Amma idan kayi a gida yafi tsafta saboda zaka rege geron ka da kyau ka tsaftace shi.Na gwada Kuma yayi kyau yayi Dadi ga gardi ga kanshi.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Gero Kofi -4
  2. Chitta busashe guda biyar
  3. Kanumfari babban chokali -1
  4. Masoro babban chokali -1
  5. Barkono guda -4
  6. Sikari dai dai bukata(optional)
  7. Ruwa dai dai bukata

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko ki surfa geron ki bakace dusar seh ki wanke ki rege tsakuwar sai ki tsameshi a colander ya tsane.Bayan ya tsane seh ki baza shi a tabarma meh tsafta ya bushe.Idan ya bushe seh ki zuba kayan kanshi ki hada a niko miki.Idan an niko seh ki tankade da rariya meh laushi.

  2. 2

    Seh ki samu mazubi meh fadi ki juye garin amma ki rage kadan.Seh ki rika yayyafawa garin ruwa kadan kadan ki cakuda da hannu zaki ga Yana dunkulewa amma da sauran gari kina gani,seh ki cigaba da cakudawa yadda zaki dunkula shi ba tare da ya fashe ba.Seh ki dunkula shi da dan girma ki aje gefe,seh ki samu tukunya ki zuba ruwa kadan ki dora a wuta ya tafasa.

  3. 3

    Bayan ruwan ya tafasa seh ki sassaka curin garin da kika dunkula a ciki idan kinga ruwan yayi yawa ya wuce qwatan curin seh ki rage kadan ba a so ruwa yayi yawa ya sha kan curin seh ki rufe ki barshi ya dahu.Idan ya dahu zaki ga bayansa yayi ja kuma ruwan yayi kauri seh ki sauke ki dakko turmi ki saka curin daya bayan daya kina dakawa Yana fashewa har ki fasa duka curin idan kinason sikari yanzu Zaki saka seki cigaba da dakawa.Seh ki dibi ruwan dahuwar kadan ki zuba a ciki ki ci gaba da kirbawa

  4. 4

    Idan ya daku ya hade jikinsa Seh ki kwashe ki cura shi iyya girman da kike so,Seh ki dakko garin da Kika rage ki saka su a ciki ko Ina ya ji.

  5. 5

    Seh ki barshi ya Sha iska.A Sha fura lafiya.

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
on
Kaduna State, Nigeria

Comments

Similar Recipes