Bhindi masala(miyar kubewa)

Wannan miya shahararriyar miya ce a qasar hindu,mafi buqatuwar kayan amfaninta su ne:kubewa,albasa,tumaturi sai kayan qamshi(spices♨️)an fi cin shi da roti(burodi)samfurin....amma ni na ci tawa da shinkafa ne qasar,yana da dadi sosai...ni da mahaifiyata mun ji dadinshi😋amma yar uwata kamar ta zaneni🤣wai abinci ga dandano har dandano ga qamshi amma na zubawa kayan yauqi😏
Bhindi masala(miyar kubewa)
Wannan miya shahararriyar miya ce a qasar hindu,mafi buqatuwar kayan amfaninta su ne:kubewa,albasa,tumaturi sai kayan qamshi(spices♨️)an fi cin shi da roti(burodi)samfurin....amma ni na ci tawa da shinkafa ne qasar,yana da dadi sosai...ni da mahaifiyata mun ji dadinshi😋amma yar uwata kamar ta zaneni🤣wai abinci ga dandano har dandano ga qamshi amma na zubawa kayan yauqi😏
Similar Recipes
-
Butter chicken
Wannan girki ya samo asali ne daga arewacin qasar hindu tun wajejen shekarun 1950s. Manyan kayan hadinshi shi ne kaza,butter da tumatur, sauran duk qari ne dan fito da dandano na musamman. Na yi wannan girki ne domin kaina. Na tashi tun ina yarinya dalilin kallon fina-finansu na fara sha'awar al'adunsu, yarukansu da abincinsu, wannan yana daya daga cikin abincinsu da nake matuqar so. Afaafy's Kitchen -
Soyayyiyar shinkafa da lemon mangwaro
#nazabiinyigirkiWannan girki na yishi ne wa Yayata wadda nake bi, lokacin tana da juna biyu ta ce tana kwadayin fried rice, ta ji dadinshi sosai dan har yanzu lokaci lokaci tana ce min tana son qara cin irinta. Abin takaicin dai 😫, yana daya daga cikin girkunan da na dauki hotunansu Daki daki daga farko har qarshe amma yanzu na rasa su sanadiyar lalacewar sdcard dina, 😥abinda ya sa jikina yin sanyi knn na ji duk daura girkin ma ya fita a kaina sbd na fi son saka cikakken recipe da hotuna. Yanzu dai haka zan daurasu ko ba cikakken ba tunda suna da yawa☹ Afaafy's Kitchen -
Soyayyar shinkafa mai nikakken nama
Godiya mai tarin yawa ga Aysha Adamawa. Na gode sosai da wannan girki da kika koyar da mu. Sosai na ji dadinshi ni da iyalina. Princess Amrah -
Miyar danyen kubewa/okro soup
Miyar kubewa miya ce mai farin jini saboda ana iya cinta da kusa kowanne abinci/tuwo sanna tanada dadin ci da kuma dandano Ayyush_hadejia -
Faten doya
Faten doya hanya ce ta sarrafa doya yadda zaaci ta da dandano mai dadi tare da ganyayyaki da sauransu. Abinci dana fara wallafawa a cookpad hausa👍😂 #jigawagoldenapron Ayyush_hadejia -
Stir fry cous cous
#sahurrecipecontest Na yini da rashin lafiya har ya zamto babu karfin yin aiki a tattare da ni. Hakan ya sa na kirkiri yin wannan cous cous din mai saukin yi kuma ga dadi a baki. Princess Amrah -
Miyar kayan lambu
Na san ba ni na fara yin irin miyar nan ba, amma dalilina na qirqirarshi a kan kaina saboda Babana ne, yana son cous cous da miyar kayan lambu, alayyahu ne ko dai ko wane irin ganye, to wannan miyar dominshi na yi musamman. Maganar gaskiya kuma sinadarin dandano da na yi amfani da shi a wannan miyar ita ce zan ce kusan sirrin fito da dandanon wnn miyar, mun ci miyar tare da dafaffen cous cous. Afaafy's Kitchen -
Gasasshen naman rago(tsire)
Tsire daya daga cikin abincin siyarwa na hanya ne da ahalina suke matuqar qauna(a taqaice dai duk wani nama😂)to an zo da nama ne da yawa da za ayi amfani ni da yar uwata a dakin girki tace gsky ya kamata ayi gashi,ni kuma nace biryani za ayi ta dage qarshe na sakar mata,ga sakamakon hkn a gabanku😁❤ Afaafy's Kitchen -
Shinkafa, miya da lemon carrot
Yana da kyau muyi anfani da kayan abincin da ke cikin lokacin su#sokotocookout Jantullu'sbakery -
Biskit mai kostad(custard)
Na kasance ina yawan ganin hanyoyin yin biskit a gurin jahun delicacies,har ya kasance da zarar naga an turo girkin biskit to nasan itace🙄amma fa banda yanzu domin kuwa bata ajiye baiwar a tare da ita kadai ba,ta koya mana kuma muna qoqarin gwadawa🤗mun gode Aunty Sadiya. Afaafy's Kitchen -
Tuwon shinkafa miya danyen kubewa
Inason tuwo Amma baina baina..Amma mr H yanason tuwo sosai zai iya ci yau yaci gobe yaci jibi😄Yayi tafiya Da zai dawo nace mai zan Dafa Masa yace tuwon shinkafa miya danyen kubewa😅 Zarah Modibbo -
-
-
Farfesun nikakken nama
#farfesurecipecontest idan mutum yana da zallar tsokar rago ko na sa baida wani tunanin da ke fado masa a rai sai ya yi farfesunshi. Toh ni a yau sai na kirki na nika naman sannan na yi farfesun nashi. Wanda nake tare da su suna ta mamaki wai ta yaya? Na ce kawai ku zura ido ku sha kallo. Da haka nake ce muku ku ma ku biyoni don jin tadda na sarrafa nawa farfesun mai matukar dadi.😂😍💃 Princess Amrah -
Gasasshen kifi da miyar kayan lambu
Wannan kifin na gasashi ne domin Yar uwata da take dauke da juna biyu tun cikin shekarar da ta gabata(ynx Alllah ya sauketa lafiya)ta nuna tana son shi ne sosai shi ne na mata irin wnn....ta nuna jin dadinta sosai,nasan kuma in kk gwada zaku yaba😉👌 Afaafy's Kitchen -
Gasasshiyar kaza
#iftarrecipecontest kamar dai yadda nake yawaita fadi a kodayaushe, cewa duk wani abu da mutun zai siya idan har ya kwatanta yinshi a gida zai ji dadinsa fiye da ni siye. Hakan ya sa nake son homemade a komai ma. Na gasa kazar ba tare da ta kone ba. Sannan kuma ta yi taushi tu6us.🤣😍 Princess Amrah -
-
-
Gasasshen nannadadden burodi mai kifi
Wannan abinci na yishi ne don siyarwa....nayi amfani da kifin gwangwani amma za a iya yinshi da kifi sukumbiya,nima dashi na saba yi yau na rasashi a inda nake shi yasa....ga yadda nayi nan a qasa ko kuma zaku amfana dashi.Ayi dahuwa cikin farinciki😊❤ Afaafy's Kitchen -
Dambun shinkafa
Ahh yau da farin cikina na fado cookpad.Wani girki da na ta6a yi 2019 ne na manta da shi kawai yau Google photos suka min notification ya cika shekara uku,ina shiga na ganshi,shi ne na tafi na duba date na kwaso sauran hotunan process din na ce bari in raba da yan uwana.Dambu mai dadin gsk da na dade ina santinshi,rana daya na yishi da dublan din da na daura a shafina na nn cookpad sanda aka yi gasar dublan(contest)har na dace da cin gasar, ina nn da gift dina a ajiye sai zani gdan miji😂. Afaafy's Kitchen -
Tsire (stick meat)
A yau da muka yi azumi na biyu ne na yi shaawar na gasa nama da kaina ba tare da na siyo gasasshe bah. Kuma abin mamaki sai na ji wanda na gasa din ma ban ta6a cin mai dadinshi bah. Yan uwa ku gwada wannan gashin na tabbata za ku ji dadinshi ku ma. Princess Amrah -
4 in 1 meatpie
Na gode sosai ga Tee's Kitchen. Na gode wa cookpad Nigeria. Da babu cookpad da ban koya kalar meatpie din nan bah. Kodayaushe ana son mutum yana canza abu. Ga shi ni ma na canza salon meatpie dina a kan wanda kowa ya sanni da shi. Princess Amrah -
Miyar bushesshen kubewa da kifi
Nayishi ne agdan mu kuma kowa yaji dadinshi sosai Ammie_ibbi's kitchen -
Kosai mai zogale
#kosairecipecontest.Saboda amfanin zogale a jikin dan Adam kama daga maganin gyambon ciki,typhoid da malaria na zabeshi domin ya zamo ganye cikin sinadaren da zanyi amfani dashi a cikin wannan girki nawa. Kwai da bakar hoda na kara wa kosai laushi da ke bayarda dadi na musamman.Dalilin wannan a koda yaushe na ke cike da marmarin kosai ba tare da gimsheni ba.Da fatar mai karatu zaya ji dadinsa bayan biyar wannan hanyoyin da zanyi bayani akai domin sarrafa kosai.Ayi girki cikin nishadi. fauxer -
Kitsattsen dublan
#FPPCNaga wannan girki tun wajen watanni 9 baya a wajen princess amrah lkcn ana cikin gasar dublan ya bani sha'awa amma sai nk jin kmr zai bani wahalar yi😩sai ynx na tattara qarfin gwiwar gwadawa......gashi dai bai samu wani hoton kirki ba amma muna godiya da gudummawarta garemu❤💥 Afaafy's Kitchen -
Dambun Couscous
#nazabiinyigirki duk wanda ya san ni ya san dambu shi ne abinci mafi soyuwa a gareni. Ina son dambu. Shi ya sa har na couscous nake yawan yi saboda yana da sauki sosai. A yau se na yi sha'awar in raba recipe dinshi tare da ku. Princess Amrah -
Tuwon shikafa da miyar wake
Wannan Abincin, sai dai nace ku tambayi nufawa yadda suke ji da shi😍😍 Reve dor's kitchen -
Shinkafa da miyar kifi da kayan lambu
Zaku ga ina yawa girka shinkafa amma to akwai dabaru na yanda za'a girka ta har a cita ku biyo ni don cin wanan girki tare da ni#katsinagoldenapron @Rahma Barde -
Dafadukar macaroni mai dankalin turawa
Duk da ban kasance mai son macaroni ba amma wannan kam na ji dadinta sosai. Iyalina sun yaba da ita har suna fatan na sake yi musu kalanshi Princess Amrah -
More Recipes
sharhai (12)