Share

Ingredients

  1. Kabeji
  2. Karas
  3. Kokumba
  4. Waken gwangwani
  5. Bama
  6. Madara ta gari
  7. Sugar, gishiri

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki yanka kabejinki ki saka shi a roba ki dan marmasa masa gishiri ki zuba ruwa ki wanke abinki, sai ki dauko gwagwa ki zuba shi a ciki ki barsa har ki gama yanka sauran kayanki domin ya tsane ruwansa.

  2. 2

    Ki dauko karas inki ki kankare dattin dake jikinsa sai ki dauko abin gugan karas ki goge shi a babban gida, daga nan sai ki dauko kokumbar ki ki yayyankata qanana qanana

  3. 3

    Ki dauko guri mai hwadi inda zaki hada kayanki, ki zuba kabejinki ciki, karas, kokumba, waken gwangwani, sugar kadan, gishiri kadan, bama. Idan kika zuba komai sai ki jujjuya sai komai ya hade jikinsa gaba daya sai ki kawo madararki ta gari ki saka sai ki qara jujjuyawa shikenan kin gama 🤤

  4. 4

    Abinda yasa muke saka gishi gurin wankin kabeji domin ya cire masa wannan warin nasa kuma ya tsane mana ruwansa

    Ana saka sugar da gishiri kadan a ciki domin suna qara fitar da dadin abin.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Aminu Aisha Buhari
Aminu Aisha Buhari @ayyush_gidadawa
on
Sokoto, Sokoto, Nigeria

Similar Recipes