Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki samu fulawa misali rabin gwangwanin Madara, se ki saka gishiri Dan kadan 👌se man zaitun 1 tablespoon, ba lallai man zaitun ba zaki iya amfani da kowanne irin mangyda, se ruwa misalin ludayi daya da rabi(a takaice de ki kwaba da Dan kauri kamar kwabin meatpia amma kar ya kaishi kauri sose)kar yayi ruwa kar kuma yayi kauri sose, se ki ajiye shi gefe, se ki zo kan kazar ki ki gyara ta ki mata hadin kayan kamshi se ki Dora ta dahu luguf ta yanda in kin saka ludayi zaki mutsuketa,

  2. 2

    Se ki samu Eggs kamar 6 se ki fasa ki yanka Albasa sose a ciki da Dan Maggi. Se ki dawo kan fulawan ki da son samu tayi 30 minutes da kwabawa, se kina gutsura kuna murza shi falen falen  (shara-shara)se ki saka shi a kwanon suya frying pan nonstick ki baza se ki debi kazar nan ki zuba dede yanda ze rufu se ki debi ruwan egg din 3 tablespoon ki zuba kan kazar se ki nade gefe daya na fulawa se ki na do dayan gefen ma se sama da kasa, kar ki manta wutan low sose zaki saka, se ki Dan diga mai,

  3. 3

    In kasan ya danyi ja se ki juya saman ma a hankali Dan kar ya bude, shima ya danyi ja, kuma kina yi kina Dan zagaye shi da mai kadan kadan Dan karya gasu yayi baki. In kin cire se ki yanka shi biyu.

    Ni memakon kaza dankali nake sawa sabo da yafi sauri kuma banson karnin ta, inayanka dankalin kananan kanana sose se in Dan saka gishiri kadan 👌 se in tafasa dankalin.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Rufaidah
Ummu Rufaidah @cook_14199821
on
Bauchi State
Tuwon Semo😍😜😗
Read more

Comments

Similar Recipes