Dambun shinkafa

Umarnin dafa abinci
- 1
Da Farko za ki Gyara shinkafa ki bayar a barzo miki ita sai ki tankade da rariyar laushi ki cire garin da tsakin za ki yi amfani ki ajiye shi agefe
- 2
Idan shinkafa ce ta waje to ki dan jika ta da ruwa mai dumi kadan idan kuma ta mu ce ta gida ki wanke kawai ki tsaneta sai ki je ki hada madambacinki wato Steamer ki zuba aciki
- 3
Ki bar su har sai sun dahu amma za ki rinka budewa kina juyawa kina yayyafa ruwa kadan dan ko ina ya dahu.Zuwa awa daya sai ki kwashe aroba Babba.
- 4
Sannan ki zo ki gyara zogale ki cire Dattin ciki ki wanke ki jika shi da ruwan dumi sai ki matse shi ki zuba akan shinkafar da ke cikin Steamer ki rufe
- 5
Sannan ki zuba Dandano da Gishiri sai ki zuba Mangyada kadan ki juya ko ina ya hadu.
- 6
Ki gyara kayan miyanki ki yi grating dinsu ki zuba akan shinkafar da kayan kanshi da ki ka daka duk ki zuba,
- 7
Sai ki mayar cikin Steamer ki rufe har sai wannan Albasa da Attaruhun kin tabbatar sun dahu basa garas garas kuma zaki ji ya fara kamshi to Steam rice na ki ya kammala.
- 8
Sai ki soya Mangyada da Albasa sosai dashi ne za a ci wannan Dambu ki hada da Yajin Maggi mai dadi ko Yajin kuli kuli ko Fish sauce ko Meat sauce duk suna dadi idan aka ci.
- 9
'Yar uwa wannan shine Yadda na ke yin Dambu kamar yadda ki ka ganshi a hoto
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
-
-
-
Dambun shinkafa
Wannan girkin shi yake wakiltata sabida ina matuqar son girki kuma dambu yanadaga cikin girkinda banjin wuyar yinshi #nazabiinyigirki hafsat wasagu -
Dambun shinkafa
Ina san dambun, kullum sai dai nayi dambun couscous ko na tsaki ban taba gwada na shinkafa ba sai yau, sai naji ashe duk yafisu dadi musamma idan yaji gyada da zogale. Ceemy's Delicious -
-
Dambun shinkafa
Dambun shinkafa abincin Hausa ne mostly, what makes special is the aroma and the texture..🤩♥️It just so sweet! sadeeya nurah -
-
-
-
-
-
-
-
-
-
-
Dambun shinkafa
Nayi wannan danbum shinkafar ne sbd me gida yn son dambu sosae Kuma Alhamdulillah yaji dadin sa sosae #WAZOBIA2 Zee's Kitchen -
Dambun shinkafa
Abincin gargajiyane mai dadi Wanda ba'a gajiya dashi a marmarce.#girkidayabishiyadaya Meenat Kitchen -
-
-
Dambun shinkafa
Shi dai dambu y kasance abinchi gargajiya wanda ake yinsa d barzazziyar shinkafa hk xalika turara shi akeyi b dafawa b yana d matukar dadi kuma ana cinsa ne a marmarce ko ayi a gidan biki ko suna mumeena’s kitchen -
-
-
-
-
-
-
-
More Recipes
sharhai