Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za'a wanke shinkafa sai a jika ta tsahon awa uku, idan ta jika sai a tsame ta daga ruwa a wanke a markada tayi laushi.
- 2
Sai a Dora ruwa kadan a tukunya a debi markadaddiya shinkafa kamar rabin cup, idan ruwan ya tafasa sai a dama kullin da aka dan diba a barshi ya sha iska sai a juye shi cikin markaden shinkafa a juya shi ya hadu sosai.
- 3
Za'a zuba yeast babban cokali daya a juya a rufe a barshi ya tashi tsahon awa biyu.
- 4
Idan ya tashi a kawo sugar a zuba da gishiri da baking powder a juya a barshi kamar minti goma zai kara tashi yayi kumfa.
- 5
Sai a dora frying pan akan wuta (non-stick) a shafa mai a ciki a debi kullin shinkafa a zuba a rufe da murfi har ya gasu, kuma ba'a juya shi. Haka za'a gasa sinasir din
- 6
Ana ci da miyar taushe ko egusi ko da sugar ko da zuma
Keywords
Similar Recipes
More Recipes








sharhai