Tura

Kayan aiki

  1. 2Shinkafa kofi
  2. Tattasai
  3. Taruhu
  4. Albasa
  5. Sinadarin dandano
  6. Kifi danye
  7. tafarnuwaGarin
  8. Curry
  9. Onga
  10. Gishiri
  11. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zakiy tafasa shinkafar ki saiki tsane ki aje gefe

  2. 2

    Daga nan zakiy blending tattasai, taruhu albasa saiki juye a tukunya ki tafasa ruwan ya tsane saiki saka mai ki soya sannan ki tsaida ruwa amma zakiy amfani da ruwa kadan saboda an tafasa shinkafar.

  3. 3

    Anan zaki juye komai na dandano cikin ruwan maggi, curry onga gishiri.

  4. 4

    Anan zaki gyara dan kifin ki, ki wanke shi yasha iska, sannan saiki saka mai a pan yayi zafi saiki soya kifin ki ki tsame idan ya soyu, saiki sake zuba mai adan pan kijuye Albasa da taruhu ki soya sama-sama ki saka dandano da curry saiki kawo kifib kijuye ki ci gaba da juyawa a hankali idan yasake laushi kisauqe

  5. 5

    Zaki koma kan ruwan shinkafar ki kijuye shinkafan sai bari ya dahu sannan ki sauqe.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
rannar
Jigawa State Nigeria

Similar Recipes