Dafa duka da kayan ciki
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki aza ruwanki akan wuta kibarsu saisun tafasa idan sukayi saikisa shinkafar ki idan ta tafasa saiki wanke sai ki aza tafasar kayan ciki ki tafasa su amman anasa musu daddano da albasa wurin tafasa
- 2
Bayan haka, Ki dauko kayan miyanki ki nikasu sannan ki dauko mai kiaza kan wuta idan ya soyu saiki sa kayan miyanki kirinka juyasu harsu soyu
- 3
Bayan haka idan suka soyu saiki dauko ruwan namanki da kayan ciki dakika dafada kayan daddano da kayan kamshi kisa
- 4
Saiki zuba ruwa Kaden cikin hadin girkinki ki kulle tukunyarki harsai sun tafasa saiki dauko tafasassar shinkafar ki kisa saiki motsa baki daya ki kulle tukunyarki don ta dahu
- 5
Idan kika tabbatar da girkinki yayi saiki saukar dashi kasa sai asa akula😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10584562




sharhai (2)