Fanke
Yayi Dadi sosai, iyalina suji dadin shi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko kisami karamin kwano, sai kizuba ruwa Rabin Kofi da yeast da sukari karamin cokali biyu ki juya ki ajiyi agefe
- 2
Sai kisami kwano kizuba fulawa da sukari da Madara da gishiri. ki duko ruwan yeast din Nan kizuba acikin fulawar ki, sai kijuyasu suhadi jikin su sosai. Sai ki rufe kibarshi kamar minti talatin.
- 3
Gashi Nan bayan yatashi sai kidura Mai a huta kizuba albada kadan idan yay zafi, sai kirinka diban kwabin fulawar ki kina zubawa acikin mai. Idan yayi sai kijuyasu Shima idan yayi sai ki kwashe
- 4
Aci Dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12543705












sharhai