Stuff potatoes

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Yau idea din ta tafi ne akan yanda ake sarrafa dankalin turawa. Ba wai kullum ki soya da kwai ba haba hajiya, sarrafashi ta wannan hanyar ki Sha mamaki. Ga Dadi ga sauki. #FPPC

Stuff potatoes

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Yau idea din ta tafi ne akan yanda ake sarrafa dankalin turawa. Ba wai kullum ki soya da kwai ba haba hajiya, sarrafashi ta wannan hanyar ki Sha mamaki. Ga Dadi ga sauki. #FPPC

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hr
2 yawan abinchi
  1. 2Dankali cin mutum
  2. Kifi yanka 2
  3. 1Kara's babba guda
  4. 1Albasa karama
  5. Maggie don dandano
  6. Curyy kadan
  7. Spices kadan
  8. Pennel seed kadan
  9. Mai cokali 2
  10. 4Kwai guda
  11. Garin burodi(bread crumb)

Umarnin dafa abinci

1hr
  1. 1

    Ga kayayyakin da muke bukata Nan.

  2. 2

    Za a fara da feraye dankali a wanke a gudansa. In so samu ne a zabo madaidiata. Sia a Sami abin kwakule dnakali a kwakule tskaiyar.

  3. 3

    Sai a Dora ruwa a zuba a dafa shi sama sama kae yayi luguf dai, Amma a kula kar a cika wuta sbd Nan da Nan yake dahuwa, idan ya tahu sai a tace a kwalanda

  4. 4

    A Dora tukunya me tsafta a zuba Mai a ciki

  5. 5

    Sannan a zuba fennel seed a juya

  6. 6

    Sai a zuba albasa a motsa na Yan mintuna

  7. 7

    Sannna a goga Kara's Bayan an kankare Bayan an wnake, a zuba a motsa

  8. 8

    Sai a kawo marmasasshen kifi shima a zuba akai

  9. 9

    A zuba kayan dandano da kayan kamshi a cigaba da soyawa har ya Zama ya soyu sai a juye a kwano

  10. 10

    Bayan ya Sha iska sai a dauko dankalin a dunga cusa hadin a cikin Ramin a hankali sbd kar ya fashe. Ayi ta Yi har a gama

  11. 11

    Sai a kada kwai a zuba Maggie da spices, a yanka albasa a saka ragowar Kara's dinnan.

  12. 12

    Sai a tsoma dankalin a ciki a jujjuya koina ya ji

  13. 13

    Sannnan a saka a cikin garin bread a jujjuya koina ya rufe

  14. 14

    Sai a sake sakawa a ruwan kwai a sa a Mai me zafi a soya. Idna yayi alamar soyuwa sai a kwashe.

  15. 15

    Masha Allah 😋😋😋

  16. 16

    Dadi sai ma kin gwada zaki banbance dadin sa da normal dankali😁😂🤣

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes