Special fried rice
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki zuba ruwan naman kazarki a tukunya saiki kara ruwa kadan daidai yacca zai dafamiki shinkafarki saiki zuba curry kadan da gishiri kadan ki juya, idan ya tafasa saiki zuba shinkafarki ki barshi ya dahu
- 2
Zaki dora pan a wuta saiki yanka albasa kanana ki zuba aciki ki zuba citta da tafarnuwa ki dinga juyawa har sai yayi laushi, dama kin dafa carrot dinki da peas saiki zuba ki zuba sweat corn kisa maggi saiki juya ki yanka green pepper da red bell pepper ki zuba
- 3
Idan yayi laushi saiki zuba shinkafarki ki juya sosai ki barshi kamar 3 minute saiki sauke,zaki iyaci da stew ko sauce
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8372600











sharhai