Hadaddar Alala(moi moi)

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

Akoda yaushe ina so naga na kirkiro wani abu daban,shiyasa na had a wannan alalar mai step kamar cake. Tayi matukar dadi sosai kuma iyalina sunyaba kwarai da gaske.kuma ku kwada zakuji dadinta sosai. #alalarecipecontest.

Hadaddar Alala(moi moi)

Akoda yaushe ina so naga na kirkiro wani abu daban,shiyasa na had a wannan alalar mai step kamar cake. Tayi matukar dadi sosai kuma iyalina sunyaba kwarai da gaske.kuma ku kwada zakuji dadinta sosai. #alalarecipecontest.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 awa da 40mnt
6shida
  1. 2kuf wake,kanana
  2. 5tattasai
  3. 9tarugu
  4. tafarnuwa3
  5. 6maggi
  6. 1/2ajino moto,ledar
  7. 1/2 tspkayan yaji
  8. 1/2kuf oil
  9. Gishiri dan dandano
  10. Lawashi yankakke
  11. Topping
  12. kwai biyu 2
  13. 2albasa kanana biyu,yankakka
  14. 2tattasai madaidata,yankakke
  15. maggi daya 1
  16. Gishiri kadan

Umarnin dafa abinci

1 awa da 40mnt
  1. 1

    Farkon abinda zakiyi shine,zaki tsince waken da kyau,sai kisa acikin turmi ki zuba ruwa kadan sai ki surfashi har sai bayan waken ya cire,sannan saeki wankeshi da kyau kitabbata kin cire bayan waken

  2. 2

    Saiki zuba ruwa acikin waken kibarshi ya jika na kamar Monti ashirin

  3. 3

    Sannan sai ki tsiyaye ruwan dake ciki,saeki saka tarugu,tattasai da kuma tafarnuwa acikin waken

  4. 4

    Sannan sai ki zuba cikin blender kimarkadashi dakyau harsai yayi laushi sosai. Zakiyi haka harki gama markada waken duka

  5. 5

    Saeki samu roba mai fadi kizuba kullun aciki,sa'annan sai ki zuba mai iya adadin da nafada

  6. 6

    Bayannan sai ki zuba,kayan yaji da maggi da kuma gishiri da ajino moto kamar yanda ake gani ahotonnan

  7. 7

    Sai ki motsashi da kyau sosai ta iyan dukkanin kayan dandanon da kikasa zai game kullun waken baki daya

  8. 8

    Sannan saiki shafa mai jikin robar da kwanon da zakiyi amfani dashi saboda kada ya kama lokacin cirewa. Saiki zuba kullun aciki kamar rabi kada yacika,saiki zuba albasa mai lawashi akai

  9. 9

    Bayan kin zuba albasa mai lawshi akai,sai kuma ki kara zuba kullun waken aciki dan saboda ya rufe lawashin. Kisamu babbar tukunya kisaka acikin saiki zuba ruwa ki rufe saiki fara dafawa kamar tsawon awa daya

  10. 10

    Bayan kin tabbatar da alalarki ta dahu,saiki fasa kwai kiyanka albasa da tarugu da tattasai kisa maggi da gishiri kadan,saiki kada kwai din

  11. 11

    Sai ki zuba kwai din aciki,ina nufin saman alalar,sai kuma ki kara rufe tukunyar dan kwan ya dahu kamar minti biyar ko goma

  12. 12

    Kamar yadda ake gani wannan alalarce bayan taa dahu,shikenan saiki zuba akan plate kingama sai ci

  13. 13

    Gashi yanda nadora alalar step,wani kan wani sai yayi kamar cake💃💃

  14. 14

    Yummy😋😋

  15. 15

    Zaki iya cin alalar da mai da yaji ko kuma sauce koma kici yanda kikeso. Sauran kullun waken da ya rage sai na kullashi aleda na dafashi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

Similar Recipes