Wainar semovita mai kulikuli

Yarana suna son wainar semovita don ko banyi ba zasu ce don Allah Mama ayi mana wainar tenda da kulikuli basu fiye son ta da tumatir da albasa ba sun Fi sonta haka.
Wainar semovita mai kulikuli
Yarana suna son wainar semovita don ko banyi ba zasu ce don Allah Mama ayi mana wainar tenda da kulikuli basu fiye son ta da tumatir da albasa ba sun Fi sonta haka.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a tankale semo Kofi uku sai a zuba yeast da dan sugar da pinch of salt aciki a kwafa kamar ta shinkafa kar tayi ruwa kar tayi tauri kuma sai a rufe asaka a rana ta tashi.
- 2
Kafin ta tashi sai a daka kulikuli tare da kayan kanshi da kayan dandandano a ajiye a gefe.
- 3
Bayan ta tashi sai a dauko tenda da mai a dora a wuta tayi zafi sai a ringa zuba Mai sai azuba kullin a ringa zuba in ya soyu sai a juya dayan barin sai a kwashe azuba a kwano sai a zuba kulikuli sai ci.
Similar Recipes
More Recipes

sharhai