Dankalin Hausa da miya😋

Steps
- 1
Da farko zaki fere dankalin ki yanka ta yadda kike son ganin ta sannan ki wanke tas ki barshi a cikin ruwan. Bayan haka sai ki sa mangyad'a a tukunyar suya ki d'aura ta akan huta. Idan mangyad'an ki ba mai wari bane toba sai kin soya ta da albasa ba.
- 2
Idan kuma mangyad'an mai wari ne to da zaran manki yayi zafi kad'an sai ki yanka albasa a ciki sannan ki dauki wani roba daban ki d'ebi dankalin d'an dai-dai yadda zai zauna a mai din ki barbad'a kishi ki guya sosai sannan ki juye a cikin mangyad'an tare da d'an yayyafa ruwa kad'an acikin mai d'in dan dankalin tayi laushi sannan ki rage wuta ya soyu a hankali.
- 3
Bayan wannan saiki gyara kayan miya ki wanke tas,sannan markad'a shi a abin markad'e amma dai kar yayi laushi,sai kisa tukunya akan wuta ki zuba mangyad'a d'an dai-dai sannan ki barshi yayi zafi saiki yanka albasa aciki idan ya d'an fara soyuwa sai ki juye kayan miyar ki a ciki.
- 4
Idan kayan miyar da ruwa zaki bari ya tsane sannan zaki iya sa kanwa idan kina tunanin zaiyi tsami sabo da tumaturin da kika saka kafin ki soya,kina soyar zaki rage wuta kisa su maggi da dai sauran kayan k'amshin da kike buk'ata kiyi ta gaurayawa har sai kinga ya soyu amma karya soyu sosai shikenan sai ki sauke bayan kin zuba dankalin ki a plate sai kisa miyar a gefe kici dad'i lfy.😍
Similar Recipes
More Recipes
-

chef Nidhi Bole
-

Lemon Dal/ Lemon Tuwar Dal For Summer
Navnita Jaiswal
-

Beena Radia
-

Kulsoom Bukhari
-

Laju Gehani
-

Namrata sarmah
-

Hema Wane
-

ifuchi
-

Boca de Fogo
-

Jarrod Milstead
-

Tara S.
-

Trisha Noble
-

Asthmeen
-

Spaghetti Jollof with Vegetables
Foodiescene/ Pat's Kitchen
-

Uma Sarkar -

Chef Alka Singh Tomar.(Blogger)
-

lusciouscenter_bysumy
-

PV Iyer
-

Theresa Cole -

Mital Viramgama
-

Dr. Sharda Sharma
-

Ugali,liver wet fry with Kales
Achieng Emilly -

Soumya Chatterje







Comments