Wainar shinkafa da miyar taushe

#1post1hope. Waina abinci ne na gargajiya ina matukar son waina sumamman inci a dinner kuma miyar taushen yaji nama da kashin tantakwashi. Uhmm its yummy.
Wainar shinkafa da miyar taushe
#1post1hope. Waina abinci ne na gargajiya ina matukar son waina sumamman inci a dinner kuma miyar taushen yaji nama da kashin tantakwashi. Uhmm its yummy.
Steps
- 1
Kwanon awo, gwangwani tara shine kwano daya, zaki jika shinkafa gwangwani takwas tsayin minti talatin ko arba'in, sai ki dafa gwangwani daya. Ki wanke shinkafar da kika jika ki sanya wanda kika dafa a ciki ki sanya yeast sai ki juya, ki yanka albasa, ki kankare danyar citta kadan ki yanka ki sanya a ciki ki kai markade.
- 2
In an kawo miki markaden ki juya sosai sai ki sanya shi wuri mai dumi ko a rana yanda zai tashi, in ya tashi zaki soya sai ki sanya baking powder a ciki ki juya ki daura tanda a wuta in ta dau zafi ki soma zuba mangyada sai ki sanya kullun wainarki. In kasan yayi ki juya saman shima yayi. Sai ki kwashe. Haka za kiyi harki gama.
- 3
Miyar taushe: zaki gyara kayan miya ki sanya citta wanda kika kankare sai ki jajjaga shi ko ki gretin, kin tafasa Nama da kayan kamshi da maggi, ki gyara gydar miya ki dakata a turmi tayi laushi ko a nika miki ita a injin nikan gyada a kasuwa wurin da kika siya, ki yanka Alaiyahu ki wanke da gishiri ki sanya a colander, ki yanka albasa slize ki wanke ki aje a gefe.
- 4
Ki daura mai a wuta ki soya albasa sai ki soya naman da kika tafasa sama-sama a ciki, sai ki sanya kayan miyar da kika jajjaga ki sanya Maggi, gishiri curry, spices ki soya kayan miyar sama-sama sai ki tsaida ruwar sanwa dai-dai yanda miyar ki ba zai yi ruwa sosai ba. Inya tafasa ki sanya gyadar miya ki barshi yayita dahuwa har ruwar miyan sai ya ragu sosai mai ya taso sama, alamar miyanki ta yi kenan.
- 5
Sai ki sanya Alaiyahu da albasa a ciki ki juya da kyau. Ki rage wutar kamar minti goma zuwa sha biyar miyarki ya kammala sai ci.
- 6
Note: banking powder yana sanya laushin waina sosai dan haka in kina bukatar tayi laushi sosai zaki iya kara shi fiye da yanda nace domin wainarki tayi laushi kamar auduga. Sannan miyar waina ba a so tayi kauri sosai, an fi so kar tayi kauri kar tayi ruwa tsaka tsaki domin yafi dadin ci da waina.
Similar Recipes
More Recipes
-

Deepa Rupani
-

Vidyutaa Kashyap
-

Sangita Vyas
-

Sampada Shrungarpure
-

Healthy Mango Oats Dryfruit Smoothie Bowl
Rita Talukdar Adak
-

ifuchi
-

Surekha Dongargaonkar
-

Nutan Shah
-

Karuna Naveen Chandwani
-

Darshana Patel
-

Adarsha Mangave
-

🌈NinjaMommaKitchen🌈
-

Beef and Barley Vegetable Soup
Jarrod Milstead
-

Chicken lollipops with honey glaze sauce😊
tanveer sayed
-

salima shafeeq
-

RUCHIKA
-

Geeta Godhiwala
-

Priya's Cooking Hub
-

Kulfa Cocktail #Ramadan special
Ammara Chaudhary
-

Ammara Chaudhary
-

Hadisa Tabassum
-

Pinkblanket's Kitchen
-

K.Madaks delicia -

Deepti Patil





Comments